|
|
"Ya ce masa, 'Ka ƙaunaci Ubangiji Jehovah-nka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka. Wannan shi ne babban umarni na farko. Na biyu kuma kamarsa yake, ‘Ka ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.’ A kan umarnin nan biyu duk Attaura da koyarwar annabawa suka rataya." Matthieu 22:37-40
"Ubangiji zai yi murna da raguna dubbai Ko kuwa da kogunan mai dubbai? Zan ba da ɗan farina ne don laifina? Ko kuwa zan ba da 'ya'yana saboda zunubina? Ya kai mutum, ya riga ya nuna maka abin da yake mai kyau. Abin da Ubangiji yake so gare ka, shi ne Ka yi adalci, ka ƙaunaci aikata alheri, Ka bi Jehovah da tawali'u." Michée 6:7-8
"Amma ku zama masu aikata maganar, ba masu ji kawai, kuna yaudarar kanku ba. Don duk wanda yake mai jin maganar ne kawai, ba mai aikatawa ba, kamar mutum yake mai duba fuskarsa a madubi, don yakan dubi fuskarsa ne kawai ya tafi, nan da nan kuwa sai ya mance kamanninsa. Amma duk mai duba cikakkiyar ka'idar nan ta 'yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai ya mance ba, sai dai mai aikatawa ne ya zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake aikatawa. In wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, sai dai ya yaudari kansa, to, addinin mutumin nan na banza ne. Addini sahihi kuma marar aibu a gaban Jehovah Ubanmu, shi ne a kula da gwauraye mata, da marayu a cikin ƙuntatarsu, a kuma a keɓe kai marar aibi daga duniya." Jacques 1:22-27
"Bayan wannan duka, makasudin maganar shi ne, ka yi tsoron Jehovah, ka kiyaye dokokinsa, gama wannan shi ne wajibi ga mutum. Jehovah zai shara'anta kowane irin aiki, ko a ɓoye aka yi shi, ko nagari ne, ko mugu." Ecclésiaste 12:13-14
|
|