Creation Science Information & Links!
Psaume 1, 51, 100 & 150
Psalms 1 • 51 • 100 • 150 - in Hausa
Psaume 1

Albarka ta tabbata ga mutumim da Ba ya karɓar shawarar mugaye, Wanda ba ya bin al'amuran masu zunubi, Ko ya haɗa kai da masu wasa da Elohim.   Maimakon haka, yana in daɗin karanta shari'ar Allah, Yana ta nazarinta dare da rana.   Yana kama da itacen da yake a gefen ƙorama, Yakan ba da 'ya'ya a kan kari, Ganyayensa ba sa yin yaushi, Yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.   Amma mugaye ba haka suke ba, Su kamar yayi suke wanda iska take kwashewa.   Elohim kuwa zai hukunta mugaye, Masu zunubi kuwa za a ware su daga adalai. 6Gama Ubangiji yana lura da al'amuran adalai, Amma al'amuran mugaye za su watse.
 

Psaume 51

Ka yi mini jinƙai, ya Elohim, Sabili da madawwamiyar ƙaunarka. Ka shafe zunubaina, Saboda jinƙanka mai girma!   Ka wanke muguntata sarai, Ka tsarkake ni daga zunubina!   Na gane laifina, Kullum ina sane da zunubina.   Na yi maka zunubi, kai kaɗai na yi wa, Na kuwa aikata mugunta a gare ka. Daidai ne shari'ar da ka yi mini, Daidai ne ka hukunta ni.   Mugu ne ni tun lokacin da aka haife ni, Mai zunubi ne ni tun daga ranar da aka haife ni.   Amintacciyar zuciya ita kake so, Ka cika tunanina da hikimarka.   Ka kawar da zunubina, zan kuwa tsarkaka, Ka wanke ni, zan kuwa fi auduga fari.   Bari in ji sowa ta farin ciki da murna. Ko da yake ka ragargaza ni, Ka kakkarya ni, duk da haka zan sāke yin murna.   Ka kawar da fuskarka daga zunubaina, Ka shafe duk muguntata.   Ka halitta tsarkakakkiyar zuciya a cikina, ya Elohim, Ka sa sabon halin biyayya a cikina.   Kada ka kore ni daga gabanka, Kada ka ɗauke mini Ruhunka Mai Tsarki.   Ka sāke mayar mini da farin ciki na cetonka, Ka ƙarfafa ni da zuciya ta biyayya.   Sa'an nan zan koya wa masu zunubi umarnanka, Za su kuwa komo wurinka.   Ka rayar da raina, ya Elohim Mai Cetona, Zan kuwa yi shelar adalcinka da farin ciki.   Ka taimake ni in yi magana, ya Ubangiji, Zan kuwa yabe ka.   Ba ka son sadakoki, ai, da na ba ka, Ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa.   Hadayata, ita ce halin ladabi, ya Elohim, Zuciya mai ladabi da biyayya, Ba za ka ƙi ba, ya Elohim.   Ya Elohim, ka yi wa Sihiyona alheri, ka taimake ta, Ka sāke gina garun Urushalima.   Sa'an nan za ka ji daɗin hadaya ta ainihi, Da dukan hadayun ƙonawa. Za a miƙa bijimai hadayu a bisa bagadenka.
 

Psaume 100

Bari dukan duniya ta raira waƙar farin ciki ga Ubangiji!   Ku yi wa Ubangiji sujada da murna, Ku zo gabansa, kuna raira waƙoƙin farin ciki!   Kada fa a manta da cewa, Ubangiji shi ne Elohim! Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne, Mu jama'arsa ne, mu garkensa ne.   Ku shiga Haikalinsa da godiya, Ku shiga wurinsa mai tsarki, ku yabe shi! Ku gode masa, ku yabe shi!   Ubangiji nagari ne, Ƙaunarsa madawwamiya ce, Amincinsa kuwa har abada abadin ne.
 

Psaume 150

Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Ku yabi Elohim a cikin Haikalinsa! Ku yabi ƙarfinsa a sama!   Ku yabe shi saboda manyan abubuwa Waɗanda ya aikata! Ku yabi mafificin girmansa!   Ku yabe shi da kakaki! Ku yabe shi da garayu da molaye!   Ku yabe shi da bandiri kuna taka rawa! Ku yabe shi da garayu da sarewa!   Ku yabe shi da kuge! Ku yabe shi da kuge masu amo! Ku yabi Ubangiji dukanku rayayyun talikai. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
 


Psalms 1 • 51 • 100 • 150
http://www.creationism.org/hausa/saPs1_51_100_ha.htm

Babba:  Harshen
www.creationism.org